Isa ga babban shafi

Turkiya za ta jagoranci aikin fitar da hatsin Rasha zuwa Afrika

Rasha ta sanar da cimma yarjejeniya tsakaninta da Turkiyya don fara aikin fitar da tan miliyan guda na hatsi ga kasashen Afrika a farashi mai rahusa, aikin da zai gudana da tallafin Qatar.

Shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya da Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya da Vladimir Putin na Rasha. © AP / Alexandr Demyanchuk
Talla

A jiya laraba ne aka cimma jituwar fara aikin jigilar hatsin na Rasha ga kasashen Afrika wanda ke da nufin saukaka farashin kayakin abinci a nahiyar da suka yi tashin gwauron zabi tun bayan da Moscow ta fice daga yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci kullawa a bara.

Ministan harkokin wajen Rasha, Alexander Grushko ya shaidawa manema labarai cewa nan gaba da kadan Turkiya za ta jagoranci aikin fitar da hatsin na Rasha wanda zai gudana bisa tallafin Qatar da ta zuba makuden kudade don ganin kasashen sun samu abincin mai araha.

A cewar ministan ba a kai ga bayyana yadda aikin jigilar hatsin zai gudana ta tekun na Black Sea ba, amma tabbas Turkiya ce za ta jagoranci aikin fitar da abincin ga kasashen na Afrika.

Rasha dai ta yi ikirarin cewa ta fice daga waccan yarjejeniyar fitar da hatsin ne saboda yadda kasashen yammaci suka karkata akalarta zuwa wadda za ta amfani manufofinsu kadai yayinda suka ci gaba da kakaba takunkumai hana fitar da hatsi da taki kan Rasha.

Tun bayan ficewa daga waccan yarjejeniya ta fitar da hatsi da aka shafe shekara guda ta na aiki bisa shiga tsakanin Turkiya da Majalisar Dinkin Duniya ne kuma Rasha ta haramta fitar da hatsin na Ukraine yayinda ta ke ci gaba da farmakar duk wani jirgin dakon kayakin abinci daya ratsa tekun na Black Sea daga Kiev.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.