Isa ga babban shafi

Korea ta Arewa ta yi damarar yaki da makwabciyarta

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un ya kori babban hafsan sojinsa, yayin da ya bukaci dakarun kasar da su kasance cikin shirin yaki tare da habbaka makamansu da kuma gudanar da jerin atisaye.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un tare da wasu mukarrabansa na soji.
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un tare da wasu mukarrabansa na soji. via REUTERS - KCNA
Talla

An dai hasko shugaban na Korea ta Arewa na zukar taba sigari a daidai lokacin da yake yi wa manyan janar-janar na sojinsa jawabi a cikin wani dakin taro.

Shugaban ya tattaunawa da dakarun nasa game da daukar matakin soji kan makwabaciyarsu Korea ta Kudu kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka rawaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na Korea ta Arewa ya ce, babban makasudin wannan taron ya ta’allaka ne kan shirin daura damarar yaki tare da tabbatar da karsashin sojojinsa na shiga filin-daga.

Taron na zuwa ne  a daidai lokacin da Korea ta Kudu da Amurka ke shirin fara gudanar da wani atisayen soji wani lokaci a cikin wannan watan na Agusta, abin da Korea ta Arewa ke kallo a matsayin shirye-shiryen afka mata, tana mai gargadin cewa, za fa ta iya mayar da mummunan martani.

A yayin taron ne, shugaba Kim ya kori babban hafsan sojinsa Pak Su , inda nan take ya maye gurbinsa da Vice Marshel Ri Yong Gil, yayin da ake ganin korarsa na da nasaba da rashin gamsuwar kwarewarsa a filin-daga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.