Isa ga babban shafi

Za mu share hanyar karbar Ukraine zuwa NATO - Stoltenberg

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce Ukraine za ta samu goron gayyatar zama mamba ne a lokacin da kawayenta suka amince da kuma cika sharuddan kungiyar.

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg kenan.
Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg kenan. REUTERS - INTS KALNINS
Talla

"Wannan zai canza hanyar zama memba na Ukraine daga mataki biyu zuwa mataki daya," in ji Stoltenberg ga manema labarai.

Shugaban na NATO ya kuma sanar da shirin bada agaji na shekaru masu yawa ga Ukraine, da kuma zaman Majalisar NATO da Ukraine, wanda za a gudanar a ranar Laraba tare da halartar shugaba Zelenskyy.

Bugu da kari, kawayenta sun amince da "tsarin tsaro mafi inganci tun bayan kawo karshen yakin cacar baka," in ji shugaban na NATO, ya kara da cewa an tsara wadannan tsare-tsare ne don tinkarar babbar barazana biyu da NATO ke fuskanta.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Khamis saleh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.