Isa ga babban shafi

WHO ta cire kyandar biri daga jerin cutukan da ke bukatar kulawar gaggawa

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce daga yanzu cutar kyandan biri, ba ta daga cikin cututtukan da ke bukatar kulawar gaggawa a duniya.

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. AP - Martial Trezzini
Talla

A watan Yulin shekarar da ta gabata, hukumar WHO ta ayyana cutar a matsayin wacce ke bukatar kulawar gaggawa a sassan duniya.

Toh sai dai bayan wani taro da kwamitin kula da cutar ya gudanar a makon nan, ya bada shawarar fidda cutar daga cikin jerin irin wadancan cutuka masu bukatar kulawar gaggawa, lamarin da shugabar hukumar Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya amince da shi.

Sai dai ya bukaci kasashe da su ci gaba da yin gwaji da kuma zama cikin shirin kota kwana don tunkarar cutar idan aka sake samun bullar ta.

WHO ta ce daga watan Janairun shekarar bara zuwa Afrilun daya gabata, sama da mutane dubu 87 ne su ka kamu da cutar, daga ciki kuwa har da mutane 140 da suka mutu a kasashe 111.

Shugaban na WHO Dr Tedros ya kuma ce an samu raguwar rahotannin kamuwa da cutar da akalla kashi 90 a cikin watanni ukun da suka gabata, idan aka kwatanta da watanni ukun can baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.