Isa ga babban shafi

China na zargin Amurka da yin amfani da tashin hankali a yankin Korea

Amurka na amfani da tashe-tashen hankula a yankin Korea wajen karfafa kawancen adawa da China,kalaman jakadan China a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP a wani lokaci da ya kai ziyara kasashen Turai.

 Liu Xiaoming Jakadan China yayin ziyara a yankin Turai
Liu Xiaoming Jakadan China yayin ziyara a yankin Turai REUTERS/Simon Dawson
Talla

Jakadan China Liu Xiaoming ya bayyana a ranar Juma'a cewa, "Sun damu matuka game da aniyar Amurka na yin amfani da matsalolin da ake fuskanta a yankin Koriya don dakile kasar China."

Jami’in ya kara da cewa, "yana daga cikin dabarunsu na Indo-Pacific,su hada kai da kawayensu, don karfafa alakarsu da Koriya ta Kudu da Japan.

Dakarun kasar China
Dakarun kasar China REUTERS - GONZALO FUENTES

Baya ga tashe-tashen hankula a yankin Taiwan, a 'yan makonnin nan ana fuskantar tashe-tashen hankula a mashigin tekun, inda arewacin kasar suka yi gwajin makami mai linzami, yayin da korea ta Kudu da kawayenta na Amurka suka shirya atisayen soji.

Pyongyang, abokiyar kawancen kasar China, ta ce a ranar Juma'a ta yi nasarar gwada wani makami mai linzami.

A watan Satumba, shugaba Kim Jong Un ya ce matsayin kasarsa na mallakar makamashin nukiliya ya kai matakin da ba za ta iya komawa baya ba.-

Shugaban China tare da Shugaban Faransa
Shugaban China tare da Shugaban Faransa via REUTERS - POOL

Washington da Seoul sun ba da hujjar atisayen nasu tare da cewa Kim ya umarci sojojinsa su kasance cikin shirin ta kwana na yakin gaske.

Bayan rangadin wasu manyan biranen Turai da suka hada da Berlin, Brussels da Paris, jakadan China Liu ya ce kamata ya yi shugabannin kasashen Turai su ja hankalin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.