Isa ga babban shafi

Akwai yiwuwar kotun ICC ta yi amfani da Afrika ta kudu wajen kame Putin

Hankulan duniya sun karkata kan Afrika ta Kudu kasar da ake ganin kotun Duniya ta ICC na shirin amfani da ita wajen kame shugaba Vladimir Putin na Rasha wanda kotun ta fitar da takardar sammacin kamen shi a ranar 17 ga watan Maris din da muka yi bakwana da shi.

Tun a ranar 17 ga watan Maris din da ya gabata ne ICC ta fitar da takardar umarnin kame Putin, wanda ke nuna cewa bashi da zarafin iya sanya kafa a wata kasa da ta yi rijista da kotun.
Tun a ranar 17 ga watan Maris din da ya gabata ne ICC ta fitar da takardar umarnin kame Putin, wanda ke nuna cewa bashi da zarafin iya sanya kafa a wata kasa da ta yi rijista da kotun. © AP/Canva
Talla

Alamomi na nuni da cewa ita kanta gwamnatin shugaba Cyril Ramaphosa na halin tsaka mai wuya lura da yadda jagoran na Moscow ke Shirin ziyartar kasar a watan Agusta mai zuwa don halartar taron kungiyar BRICS.

Karkashin dokokin kotun hukuntan manyan laifukan ta ICC wadda Afrika ta kudu ke matsayin mamba a cikinta, wajibi ne kasar ta mika duk wani da kotun ke nema da zarar ya sanya kafa a Pretoria, lamarin da ke matsayin babbar damuwa ga ziyarar ta Putin.

Tun zamanin mulkin Nelson Mandela a shekarun 1988 Afrika ta kudu ke karkashin kotun ta Duniya tare da mutunta hukunce-hukuncenta, sai dai ana ganin abu ne mai wuya kasar ta amince da zama sanadin mika Putin lura da alakar Rasha da kasar.

Ministan da ke kula da alakar kasar da ketare, Naledi Pandor ya shaidawa manema labarai cewa yanzu haka suna tattaunawa don samun haske kan yadda za su tunkari wannan matsala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.