Isa ga babban shafi

Kasar Cuba ta yi tir da takunkumin da aka kakabawa Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Cuba Miguel Diaz-Canel sun kaddamar da wani mutum-mutumi don tunawa da jagoran juyin juya hali na Cuba Fidel Castro, inda suka yi alkawarin kara dankon zumuncin da ke tsakaninsu dangane da takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasashen biyu.

Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel tare da takwaransa na rasha Vladmir Putin
Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel tare da takwaransa na rasha Vladmir Putin © Wikipedia
Talla

Yayin tunawa da irin gudun mowar da Castro ya bayar, Putin shaidawa Diaz-Canel cewa kasashen biyu na bukatar su kara gina "tushen abokantaka" da aka kafa tsakanin Castro da shugabannin Soviet.

Diaz-Canel ya yi Allah wadai da takunkumin da aka kakabawa Rasha, ya kuma ce, “Cuba na adawa da matakin da aksashen yamma suka dauka akan kasar bisa rashin adalci.

"Dole ne a gano musabbabin rikice-rikicen da ke faruwa a wannan yanki a cikin manufofin Amurka masu tayar da hankali da kuma yunkurin fadada NATO zuwa kan iyakokin Rasha, wanda Cuba ta yi tir da shi.

Ya kara da cewa "Cuba, kamar yadda ta bayyana a lokuta da dama, tana goyon bayan tattaunawar sulhu don warware rikicin da ake ciki yanzu."

Shugaban ya ce shakka babu kasarsa za ta ci gaba da karfafa alakar da ke tsakaninta da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.