Isa ga babban shafi

Duniya ta samu karin yunwa da fin kashi 100 saboda dumamar yanayi -Oxfam

Wani rahoton Oxfam, da ya yi kira ga kasashe masu arziki su rage hayakin da su ke fitarwa, tare da biyan diyya ga kasashe masu karamin karfi, ya ce bala’in yunwa ya karu da sama da kashi 100, a yankunan da suka fi fama da matsalolin sauyin yanayi a sassan duniya.

Rahoton na Oxfam ya ce matsalar dumamar yanayi kai tsaye ta yi mummunar illa ga harkokin noma a kasashe da dama.
Rahoton na Oxfam ya ce matsalar dumamar yanayi kai tsaye ta yi mummunar illa ga harkokin noma a kasashe da dama. REUTERS/Yusuf Ahmad
Talla

Binciken da Oxfam ta yi wa taken, "Yunwa a cikin duniya mai fama da dumamar yanayi," ya gano cewa matsananciyar yunwa ta karu da kashi 123 bisa 100 cikin shekaru shida a kasashe goma da suka fi fama da matsalar sauyin yanayi.

Kasashe goma da suka fi fama da matsalolin sauyin yanayi, kama daga fari da ambaliyar ruwa cikin shekaru 20 da suka gabata zuwa yanzu sun hada da Somalia, da Haiti, da Djibouti, da Kenya, sai Nijar, da Afganistan, da Guatemala, sai kuma Madagascar, da Burkina Faso da Zimbabwe.

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya WFP ta ce, kimanin mutane miliyan 48 a fadin kasashen da aka ambato ne bincike ya gano suna fama da matsananciyar yunwa.

Wannan adadi na mutane miliyan 48 ya karu ne daga miliyan 21 da aka gano sun fama da yunwa a shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.