Isa ga babban shafi
Najeriya-Kare

Najeriya ce ta 3 a sahun kasashen da suka fi cin naman kare

Wani binciken masana ya bayyana cewar Najeriya ce kasa ta 3 da aka fi cin naman kare a duniya, bayan kasashen Koriya ta Kudu da Vietnam.

Naman karen dai yana da matsayi sosai a wasu jihohin kudancin Najeriya da suka hada da Akwa Ibom da Cross Rivers da kuma Rivers.
Naman karen dai yana da matsayi sosai a wasu jihohin kudancin Najeriya da suka hada da Akwa Ibom da Cross Rivers da kuma Rivers. © RFI Hausa
Talla

Rahotan binciken da Mathew Nash ya jagoranta wanda Jaridar Premium Times ta wallafa yayi karin haske akan kasashen da kiwon karnuka ke da tasiri da akasin haka a wannan shekara ta 2022.

Rahotan ya ce duk da ya ke ana matukar cin naman karan lokacin bukukuwa a China, kasar bata cikin jerin kasashe 3 na duniya da akafi cin naman karan kamar yadda binciken da aka gudanar a kasashe 51 ya nuna.

Wannan binciken ya mayar da hankali ne akan kasashen da ake kare hakkin karnukan da kasashen da ake barin karnukan su shiga otel-otel da wadanda ke da isassun likitocin dake kula da su da masu kungiyoyin kare hakin dabbobi da masu fama da barazanar kamuwa da cutar cizon karnukan da kuma wadanda ke da dokar alaka tsakanin dabbobi da mutane.

Najeriya ta zo ta 45 daga kasashe 51 da suka cika mizanin binciken da aka gudanar da maki 44.41, yayin da Italia ke matsayi na farko sai New Zealand sannan Faransa da Birtaniya da Jamus.

Duk da matsayin Najeriya na zama kasa ta 3 da aka fi cin naman karen, a watan Yulin bara akalla mutane 18,000 suka sanya hannu akan wata takardar korafi inda suka bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin sa da su haramta cin naman karen da kuma sayar da shi.

Naman karen dai yana da matsayi sosai a wasu jihohin kudancin Najeriya da suka hada da Akwa Ibom da Cross Rivers da kuma Rivers inda aka masa lakabi da 404.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.