Isa ga babban shafi
HIV-Holland

An gano wani nau'in cutar HIV a Netherlands

Masu bincike a jami’ar Oxford sun fitar da sanarwar gano wani sabon naucin kwayar cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki a Kasar Netherlands.

Fiye da mutane miliyan  ke fama da  HIV, kwayar cutar da ke kawo AIDS.
Fiye da mutane miliyan ke fama da HIV, kwayar cutar da ke kawo AIDS. AFP/File
Talla

Bayanan da Masu binciken na jami’ar Oxford suka fitar a jiya Alhamis na cewa garkuwar jikin wadanda suka harbu da sabon nau’in kwayar cutar da ake kira VB VARIANT yana da rauni, kuma suna da ninki 3.5 zuwa ninki 5.5 na kwayar cutar a jinin jikin su.

Kazalika binciken ya kuma gano bayan fara shan magani, warkewar masu dauke da kwayar VB  ya banbanta da na wadanda aka sani a da.

Sai dai a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa, Chris Wymant wani kwararre a jami’ar ta Oxford ya ce kowa yayi karatun ta natsu da bullar sabon nau’in cutar ta HIV, bugu da kari, ya ce ba wani abin daga  hankali.

Cutar ta HIV dai ta bulla ne a karshen shekarar 1980 a Kasar Netherlands, sai dai adadin yaduwarshi ya zaftare a cikin shekarar 2010 kamar yadda masu bincike suka bayyana.

Cutar ta HIV ta shafe gomman shekaru tana bazuwa a kasar da al’ummarta suka bayyana kwanciyar hankali da zaman cutar a tattare dasu ganin yadda magungunan da ke akwai na karya kaifin ta.

Wannan rahoto dai na zuwa ne a daidai lokaci da duniya ke fama da annobar coronavirus da yayi ta’adi a bangarorin rayuwa dabam dabam na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.