Isa ga babban shafi
'YANCIN-JARIDA

RSF tace 'Yan Jaridu 488 ake tsare da su a kasashen duniya bana

Kungiyar 'Reporters Without Borders' ko kuma RSF dake sanya ido akan harkokin da suka shafi ayyukan ‘Yan Jaridu a duniya tace yanzu haka ma’aikatan yada labarai 488 ke garkame a gidajen yari daban daban na duniya, wanda shine adadi mafi yawa da aka gani a cikin shekaru 25

Rahotan kungiyar RSF
Rahotan kungiyar RSF © RSF
Talla

Sanarwar kungiyar ta bayyana cewar ‘Yan Jaridu 46 aka kashe a wannan shekara ta 2021 wanda shine kuma adadi mafi karanci tun lokacin da ta fara gabatar da rahoto akai.

Kungiyar dake fafutukar tabbatar da ‘yancin ‘Yan Jaridu wajen gudanar da ayyukan su ba tare da tsangwama ba tace tun daga shekarar 1995 ba’a taba samun shekarar da aka garkame ‘Yan Jaridu da yawa a gidan yari irin na bana ba, adadin da tace ya karu da kashi 20 daga wanda aka gani bara.

RSF tace adadin ‘Yan Jaridu mata da aka tsare bana ya kai 60 sabanin wanda aka gani a shekarar 2020.

Kasar China ke sahun gaba wajen garkame ‘Yan Jaridu a gidan yari wadanda yawan su ya kai 127, matakin dake yiwa dimokiradiyar kasar zagon kasa, yayin da Myanmar ke matsayi na 2 da ‘Yan Jaridu 53 sai Vietnam mai mutane 43, kasar Belarus na da ‘Yan Jaridu 32 sai kuma Saudi Arabia mai mutane 31.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.