Isa ga babban shafi
Cop26

An gaza cimma matsaya a taron yanayi na duniya tare da tsawaita shi

An tsawaita taron sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya COP26 dake gudana a Glasgow har zuwa wannan Asabar, bayan da aka gaza cimma matsaya kan matakin karshe na rage gurbatacen iska, inda ranar Juma'a shugaban taron Alok Sharma ya yi kira ga kasashe da su yi kokarin karshe na tabbatar da alkawurran da za su iya shawo kan yanayin zafi da ke barazana ga duniya.

Dakin taro kan sauyin yanayi dake gudana a Glasgow na kasar Scothland 11/11/21.
Dakin taro kan sauyin yanayi dake gudana a Glasgow na kasar Scothland 11/11/21. Paul Ellis AFP
Talla

Shugaban taron na COP26 Sharma wanda yace "Duniya na sa’ido a kansu," ya bayyanawa wakilan da aka dorawa alhakin kiyaye manufofin dumamar yanayi dake cikin yarjejeniyar birnin Paris da su dauki mataki dubu da bala'o'in da yanayi ke haifarwa a kasashen duniya.

Sharma ya ce yana sa ran za a ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar har zuwa yammacin wannan  Asabar yayin da wa'adin ranar 12 ga watan Nuwamba ya wuce ba tare da cimma yarjejeniya ta karshe ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.