Isa ga babban shafi
Cuba - Korona

Cuba za ta yi wa kananan yara rikafin korona don bude makarantu

A wani sharadin sake bude makarantu a kasar Cuba, gwamnatin kasar ta kaddamar da wani Shirin soma yiwa yara masu shekaru biyu zuwa 18 allurar rigakafin annobar Covid-19 dake kara ta’azzara.

Yadda hukumomin Cuba suka fara yi wa yara allurar rigakafin korona kafin bude makaruntu 24/08/21
Yadda hukumomin Cuba suka fara yi wa yara allurar rigakafin korona kafin bude makaruntu 24/08/21 AP - Ramon Espinosa
Talla

Yara masu shekaru 12 zuwa sama za su kasance rukunin farkon na waɗanda za su karɓi ɗaya daga cikin alluran rigakafin korona guda biyu da aka samar a cikin gida, wato Abdala da Soberana, sai kuma ƙananan yara masu kasa da shekaru 12 su biyo baya.

Tun a cikin watan Maris na shekarar 2020 hukumomi suka rufe akasarin makarantu, inda ɗalibai suka fara daukar darussa ta kafofin talabijin, kuma haka matakin zai ci gaba, ko bayan bude makarantun a wannan Litinin har sai yi wa duk yaran da suka cancanta allurar rigakafi.

Laura Lantigua, wata 'yar shekara 17, na makarantar sakandaren Saul Delgado da ke Havana babban birnin Cuba, ta karbi allurar farko cikin cikin uku da ya kamata a karba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.