Isa ga babban shafi
Amurka-Cuba

Za mu yi amfani da karfi don taimaka wa jama'ar Cuba-Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana nazarin amfani da karfi wajen samar da hanyoyin sadarwar intanet ga jama’ar kasar Cuba sakamakon matakin da hukumomin kasar suka dauka na katse sadarwar saboda zanga-zangar jama’a.

Shugaba Joe Biden na Amurka
Shugaba Joe Biden na Amurka SAUL LOEB AFP
Talla

Yayin jawabi ga manema labarai bayan ganawar da suka yi da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da ke ziyara a Amurka, Biden wanda ya bayyana Cuba a matsayin kasar da ta gaza, take kuma ci gaba da tirsasa wa jama’arta, ya ce ba zai dauki matakan gaggawa wajen janye dokar da ta hana 'yan Cuba da ke Amurka aikewa da kudade gida ba domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Shugaban ya ce suna duba hanyar taimaka wa jama’ar kasar wajen samar musu da hanyar sadarwar intanet, inda masana ke cewa za a iya aikewa da balan-balan mai dauke da Wifi kamar yadda ake a yankunan da aka samu annoba.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta mayar da hankali ne akan bala’in ambaliyar da ta afkawa kasarta, inda ta ce zuciyarta ta koma gida, yayin da take jajanta wa wadanda suka rasa 'yan uwansu.

Merkel ta sha alwashin taimaka wa wadanda iftila’in ya ritsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.