Isa ga babban shafi
Venezuela

Fada tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga a Venezuela ya hallaka mutane da dama

Jami’an tsaron Venezuela sun kutsa kai wasu unguwannin  marasa galihu hudu na Caracas babban birnin kasar ranar Juma’a, a kokarin kawo karshen rikicin da ya shiga kwanaki biyu tsakaninsu da kungiyoyin da ke dauke da muggan makamai, lamarin da ya lakume rayukan mutane da dama.

Wani jami'an tsaron Venezuela yayin samame a birnin Caracas a watan Afrelun 2019.
Wani jami'an tsaron Venezuela yayin samame a birnin Caracas a watan Afrelun 2019. STR AFP/File
Talla

Wani jami'in ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa "su ke iko da anguwannin, to saidai yana mai cewa har yanzu akwai wasu 'yan bindiga dadi dake labe"

Hukumomin kasar basu bayyana adadin wadanda suka mutu ba tsakakin bangarorin biyu, sai dai kafofin yada labaran cikin gida sun ce gomman mutane sun rasa rayukansu tun lokacin da fada ya barke tsakanin ‘yan dabar da kuma ‘ yan sanda.

A ranar Alhamis, hukumomi sun ba da sammacin bincike tare da bayar da tukuicin da ya kai $ 500,000 ga duk wanda ya gano shugabannin kungiyoyin 'yan dabar da suka haddasa mummunan rikicin, amma kuma suka buya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.