Isa ga babban shafi
MDD

Masu zaman kashe wando za su karu-Rahoto

Majalisar Dinkin Duniya tace za a samu Karin marasa ayyukan yi miliyan 11 a duniya a shekaru biyar masu zuwa saboda tsaikon da ake samu wajen ci gaba. Rahotan Majalisar yace nan da shekara 2019 marasa ayyukan yi zasu kai miliyan 212 a fadin duniya sabanin miliyan 201 da ake da shi yanzu haka.

Matsalar rashin aiki yi a Afrika
Matsalar rashin aiki yi a Afrika Reuters
Talla

Shugaban kungiyar kwadago ta duniya Guy Ryder ya danganta matsalar da ake samu wajen ci gaban tattalin arziki.

Hukumar kwadagon ta duniyaa tace akwai bukatar a samar da ayyukan yi miliyaan 280 kafin 2019 domin cige gibin matasalar tabarbarewar tattalin arziki a duniya.

Rahoton yace an samu ci gaba a kasashen Amurka da Japan da Birtaniya tare da bayyyana cewa matsalar na ci gaba da karuwa a wasu kasashen Turai.

Matakan tsuke bakin aljihu dai na daga cikin dalilan da suka haifar da matsalar karuwar rashin aikin yi musamman a Turai.

Rahoton yace za a samu karuwar rashin ayyukan yi a Jamus da Faransa daga nan zuwa 2017. Kuma rahoton yace matsalar rashin ayyukan yi tafi shafar matasa ‘yan shekaru tsakanin 15 zuwa 24.

Haka kuma rahoton yace matsalar za ta shafi kasashen latin Amurka da Nahiyar Afrika da Asia saboda matsalar faduwar farashin danyen mai da aka samu a kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.