Isa ga babban shafi
Syria-Iraq-MDD

Kwamitin tsaro na MDD ya zargi zasu yan kasashen Saudiya da Kuwait da tallafawa mayakan jahadin kasar Iraki

Kwamitin tsaro na MDD ya amince da wani kudirin ba tare da hamaya ba, na harmta daukar mayaka tare da bada tallafin kudi ga kungiyoyin mayakan jahadi a kasashen Syriya da Iraki

REUTERS/Carlo Allegri
Talla

komitin ya saka sunayen wasu mutane 6 da suka hada da shuwagabanin kungiyar Islama ta Alnusra, yan kasashen Saudiya da Kwait a cikin jerin sunayen wadanda takunkumin kasashen duniya yahau kansu, sakamakon alakar da suke da ita da kungiyar Alkaida

Matakin ladabtarwar da MDD ta dauka a kan wadannan mutane 6 dai , ya hada ne da karbe kaddarorin da suka mallaka a kasashen ketare tare da haramta masu tafiye tafiye

Kudirin da kasar Britaniya ta bada shawarar dauka shine dai wanda ya fi zama dai dai kuma jiran ganin kwamitin tsaron ya dauka, dangane da yadda mayakan jahadin kungiya EI masu fafatukar kafa kasar Musulunci a Iraki, ke ci gaba da samun nasara, inda yanzu haka take rike da yankuna masu yawa a yankin kan iyakokin kasashen Syriya da Iraki, inda suke ci gaba da tabka ta’asar kisan jama’a a wadannan yankunan 2
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.