Isa ga babban shafi
Saudiya

Gobara Ta Hallaka Mutane 13 A Saudiyya

Hukumomi  a kasar Saudiyya na cewa mamata sakamakon gobara da ta tashi daren jiya a wani Otel dake yammacin birnin Madina, sun kai 13.A jiya Hukumomin kasar sun ce mutane 15 ne suka mutu amma kuma  yau sun bayyana cewa ba haka ne ba.Ofishin jakadancin kasar Masar a Jedda yace mamata tara ‘yan kasar Masar ne, cikin su akwai yara kanana biyu.Bayanai na cewa mutane sama da 130 suka sami raunuka yawanci sakamakon shakar hayaki daga gobaran. 

Sarki Abdallah na Saudiya
Sarki Abdallah na Saudiya rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.