Isa ga babban shafi
Syria-Geneva

An bude taron sulhunta rikicin Syria a Montreux

Bayan shafe shekaru uku ana yaki a Syria, a yau Laraba ne manyan shugabannin kasashen duniya suka jagoranci zaman sulhu tsakanin gwamnatin Bashar al Assad da ‘Yan adawa da ke yaki da shi domin kawo karshen rikicin kasar da ya lakume rayukan mutane sama da dubu dari.

Lakhdar Brahimi da John Kerry da Ban Ki-moon da Sergueï Lavrov, à taron sasantawa rikicin Syria a Montreux
Lakhdar Brahimi da John Kerry da Ban Ki-moon da Sergueï Lavrov, à taron sasantawa rikicin Syria a Montreux REUTERS/Gary Cameron
Talla

Wannan ne karon farko da za’a zauna tsakanin wakilan gwamnatin Syria da kuma na ‘Yan adawa a Geneva.

Babban batun da zai mamaye zaman taron shi ne makomar Bashar al Assad inda muradin ‘Yan adawa shi ne shugaban ya yi murabus domin kafa gwamnatin rikon kwarya.

Amma tun kafin ranar soma taron na yau, shugaban Syria, Bashar al Assad yace babu abinda zai kawar da shi daga mulkin, yana mai neman kasashen duniya su fito da hanyoyin yaki da Yan ta’adda a Syria.

Cikin wadanda suka jagoranci zaman sasantawar akwai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki moon da Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwarnsa na Rasha, Sergei Lavrov da Brahimi babban mai shiga tsakanin rikicin Syria da kuma wakilan wakilan kasashe sama da 30 yawanci na kasashen Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.