Isa ga babban shafi
Syria-Geneva

Baraka ta kunno kai a yunkurin sasanta rikicin Syria a Geneva

Baraka ta kunno kai a yunkurin da kasashen Duniya ke yi na sasanta rikicin Syria inda babbar kungiyar adawar Syria ta yi watsi da kudirinta na halartar taron bayan shugaba Bashar al Assad yace zai iya sake neman wa’adin shugabanci da kuma goron gayyata da Majalisar Dinkin Duniya ta ba Iran.

Shugaban kasar Syria, Bashar al - Assad a lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillacin Labaran Faransa
Shugaban kasar Syria, Bashar al - Assad a lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP PHOTO / HO / SYRIAN PRESIDENCY MEDIA OFFICE
Talla

Shugaba Assad ya shaidawa Kamfanin dillacin Labaran Faransa cewa yana da yakinin zai sake neman wa’adin shugabanci.

Gwamnatin Iran da ‘Yan adawa ke zargin tana marawa Assad baya, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yace akwai rawar da Iran za ta taka a zaman tattaunawar domin samun zaman lafiya a Syria. Babbar Kungiyar ‘Yan adawa tace zata kauracewa taron na Geneva.

Kakakin ‘Yan adawar Louay Safi, yace ba zasu halarci taron ba har sai Ban Ki-moon ya janye goron gayyatar da ya ba Iran.

Amurka da Birtaniya da Faransa sun ce akwai bukatar Iran ta fito fili ta amince da kudirin da ake son cim ma na kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya idan har tana son halartar taron.

Kasar Rasha dai tana ganin rashin halartar kasar Iran a zaman taron babban kuskure ne, amma kasar Saudiya da ke goyon bayan ‘Yan adawa ta yi watsi da wakilcin Iran a zaman taron.

Shugaba Assad wanda zai aika da wakilansa ya nemi babbar ajandar taron da za’a gudanar a Montreux a kasar Switzerland ta kasance yaki da ta’addanci a Syria yana mai jaddada kudirinsa na tsayawa takarar zabe a watan Juni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.