Isa ga babban shafi
Italiya

Wasu bakin haure 'yan Afrika sun sake isa Italiya

Wasu bakin haure da yawansu ya kai 180 mafi yawansu daga nahiyar Afirka sun isa a tsibirin Lampe-dusa, mallakin kasar Italiya a cikin wasu kananan jiragen ruwa, a kokarinsu na shiga nahiyar Turai. Jirgi na farko dai na dauke ne da mutane 90 cikinsu har da mata 14 dukkaninsu ‘yan Somaliya, yayin da wani karamin jirgin ruwa dauke da mutane 84 da suka hada da mata tara, suka iso a cikin wani jirgin na daban dukkaninsu a cikin yanayi na gajiya. 

Wasu bakin haure a tsibirin Lampedusa
Wasu bakin haure a tsibirin Lampedusa AFP/Roberto Salomone
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.