Isa ga babban shafi
Gabon

Masu fashi a kan teku sun karbe wani jirgin mai a kusa da gabar tekun Gabon

Masu fashin jiragen ruwa a saman teku sun karbe wani jirgi da ke dauke da mai a kusa da gabar tekun kasar Gabon. An dai karbe jirgin ne tare da akalla mutane 24 wadanda dukkaninsu indiyawa ne; ciki harda matukan jirgin. 

Wani jirgi da 'yan fashin teku na Somaliya suka kwace
Wani jirgi da 'yan fashin teku na Somaliya suka kwace
Talla

Rahotanni na kuma nuna cewa jirgin na nan a yankin ruwan Najeriya a cewar hukumomin kasar ta Gabon.

Wannan kuma shine karo na farko da hakan ta auku a wannan yanki duk da irin fashin jiragen da ake fama da shi a mashigar ruwan Guinea dake Yammacin Afrika.

Rahotanni na nuna cewa 'yan fashin wadanda yawansu aka yi kiyasin ya kai 12 zuwa 15 sun farma jirgin ne dauke da manyan makamai.

A dai farkon wannan mako hukumar kasa da kasa dake kula da zirga zirgar jirage ta yi kashedin cewa mashigar ruwan Guinea wadda aka fi sani da ayyukan fashin jirage ta fara zama wani yanki da ake yin garkuwa da mutane a wannan shekara.

Ko a watan da ya gabata ma hukumar dake yaki da fashin jirage ta saka sunan yankin ruwan kasar Togo a cikin yankunan da suka fi hadarin safara akan teku da suka hada har ila yau da Najariya da kuma Jamhuriyar Benin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.