Isa ga babban shafi
Amurka-Uganda

Obama ya tsawaita wa’adin dakarun Amurka a Uganda domin farautar Kony

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kara wa’adin dakarun kasar da ke taimakawa Sojan Uganda farautar madugun ‘Yan tawaye Joseph Kony wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin cin zarafin kanana yara.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama
Shugaban kasar Amurka Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Talla

A bara ne Shugaba Obama ya aika da dakarun Amurka 100 a Uganda domin taimaka wa dakarun kasar farautar Joseph Kony, madugun ‘Yantawaye LRA.

Joseph Kony yana cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo a duniya, saboda sace yara da azabtar da su, da tilasta masu shiga aikin soja, tare da daddatse wasu sassan jikinsu.

Shugaba Obama yace taimakon da Amurka zata bayar ke nan domin ganin an cafek Mista Kony

Dakarun Amurka tare da hadin gwiwar dakarun Uganda sun kaddamar da bincike tare da yaki da ‘Yan Tawaye a daji mai tsawon kilomita 400 a yankin kasar da tsakiyar Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.