Isa ga babban shafi

Babban hafsan sojin Kenya ya mutu a hatsarin jirgin sama

Shugaba William Ruto na Kenya, ya sanar da cewa babban hafsan sojin kasar, Janar Francis Ogolla, na cikin mutane 10 da suka mutu a lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya yi hatsari jim kadan bayan tashinsa a ranar Alhamis.

Akalla sojoji 10 ne suka mutu a watan Yunin 2021 lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya yi hatsari a lokacin da yake sauka kusa da babban birnin kasar Nairobi.
Akalla sojoji 10 ne suka mutu a watan Yunin 2021 lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya yi hatsari a lokacin da yake sauka kusa da babban birnin kasar Nairobi. © Reuters
Talla

Jirgin wanda ya kai ziyara ga sojojin da aka tura a arewa maso yammacin Kenya domin yaki da matsalar satar shanu, ya sauka ne 'yan mintoci kadan bayan barin makarantar sakandare ta Cheptuel Boys da ke gundumar Pokot ta Yamma.

Bayanai sun ce, sojoji biyu ne suka tsira da rayukansu, kuma suna kwance a asibiti, inda tuni aka aika da tawagar bincike ta sama domin gano musabbabin hatsarin.

A baya Ogolla shi ne shugaban rundunar sojin sama ta Kenya, kafin ya zama mataimakin hafsan soji, kafin daga bisani shugaba Ruto, ya ba shi mukamin babban hafsan sojan kasar a shekarar da ta gabata.

Ya shiga aikin sojan Kenya ne a shekarar 1984, inda ya samu horo a matsayin matukin jirgi na yaki tare da sojojin saman Amurka da kuma matsayin malamin matukin jirgi a rundunar sojin saman Kenya, a cewar bayanan ma’aikatar tsaro.

An kashe fararen hula da jami'an 'yan sanda da dama a rikicin da ya barke tsakanin masu satar shanu, a yankin arewa maso yammacin kasar.

Akalla sojoji 10 ne suka mutu a watan Yunin 2021 lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya yi hatsari a lokacin da yake sauka kusa da babban birnin kasar Nairobi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.