Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Faransa uku

Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Faransa guda uku, bisa zarginsu da yiwa kasar zagon kasa.

Kofar ofishin jakadancin Faransa da ke Ouagadougou wanda masu zanga-zangar goyon bayan juyin mulkin soja suka lalata ta, ranar 3 ga Oktoba, 2022.
Kofar ofishin jakadancin Faransa da ke Ouagadougou wanda masu zanga-zangar goyon bayan juyin mulkin soja suka lalata ta, ranar 3 ga Oktoba, 2022. © AFP
Talla

Jami'an diflomasiyyar da suka hada da masu ba da shawara kan harkokin siyasa biyu, an ba su wa'adin sa'o'i 48 da su fice daga kasar, duk da cewa gwamnatin bata bayyana takamaiman abubuwan da take zargin su a kai ba, illa zagon kasa.

Wannan matakin ya kara dagula dangantaka tsakanin Burkina Faso da Faransa tun bayan da sojoji suka karbi mulkin kasar a shekarar 2022.

A baya dai gwamnatin mulkin sojin ta kori sojojin Faransa, tare da sallamar jakadan Faransa da ke kasar, inda kuma ta dakatar da wasu kafafen yada labaran kasar da ta yi mata mulkin mallaka a baya.

Rahotanni daga kasar dai na cewa, sallamar Faransawan na da nasaba ne da zaman tattaunawar da suka yi da wasu kungiyoyin fararen hula.

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta fuskanci suka kan yadda take murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki, a daidai lokacin da ake fuskantar kalubalen tsaro daga kungiyoyin ‘yan ta’adda masu alaka da Al Qaeda da IS.

Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta yi watsi da zargin da ake musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.