Isa ga babban shafi

Shugaban Senegal ya kaddamar da majalisar zartaswar gwamnatinsa

Sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya fara kaddamar da sabbin mambobin majalisar zartaswar sa, a gwamnatin da ya yiwa lakabi da “mikakkiyar hanya”.

Shugaban kasae Senegal Bassirou Diomaye Faye
Shugaban kasae Senegal Bassirou Diomaye Faye AFP - JOHN WESSELS
Talla

Mai shekaru 44, wanda bai taba rike wani mukamin gwamnati ba Mr Diomaye, ya nada Ousmane Sonko kuma madugun adawar kasar a matsayin Prime minister, sai kuma Birame Souleye Diop da aka nada a matsayin ministan lantarki, ma’aikata mai matukar muhimmanci a kasar.

Ana kuma sa ran Diop din ne zai sanya idanu a fannin samarwa da kuma sarrafa mai da Iskar gaz da kasar  zata fara aikin sa a bana.

Haka kuma Faye ya nada Ousmane Diagne tsohon mai shigar da kara na babar kotun Dakar a matsayin ministan Shari’a.

Akwai mata hudu da aka mika musu ma’aikatun harkokin waje, kiwon kifi, iyali da matasa da kuma ma’aikatar kula da al’adu.

A yanzu abinda matasan kasar suka zagu su gani shine tanadin da gwamnati ta yi musu, la’akari da rashin aikin yi da yayi musu katutu, dalili kenan da ya sanya sabon shugaban shan alawashin shigar da matsa cikin gwamnatin sa da kuma inganta rayuwar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.