Faye ya nada Ousmane Sonko a matsayin Firaministan Senegal
Sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya nada Ousmane Sonko mukamin Firaminista a kasar ta yammacin Afrika, wanda ke matsayin tsohon ubangidansa kuma tsohon dan takarar shugabancin kasa da ya yi takun-saka da tsohon shugaba Macky Sall.
Wallafawa ranar:
Jim kadan bayan kammala shan rantsuwar fara aiki ne shugaba Faye ya sanar da nadin Sonko a matsayin Firaminista kuma tuni tsohon babban abokin gabar na Macky Sall ya amsa mukamin tare da bayyana shirinsa na mika sunayen ministocin da ya ke shirin kafa majalisa da su.
Babu dalilin da zai hana ni karbar mukamin Firaminista
A jawabinsa na karbar mukamin na Firaminista, Sonko ya ce bai ga dalilin da zai hana shi karbar mukamin ba, maimakon haka yanzu ne lokacin da ya kamata ya mara baya ga Faye don ganin ya samu nasara a mulkinsa musamman wajen cika alkawurran da ya daukar wa al’ummar Senegal.
Sabon shugaban kasar na Senegal da ke matsayin mafi karancin shekaru a tsakanin takwarorinsa na nahiyar Afrika, bai taba rike wani mukamin gwamnati ba gabanin nasarar ta lashe zaben shugaban kasa kwanaki 10 bayan fitar shi daga Yari.
Tsawon shekaru 2 Sonko mai shekaru 49 ya shafe yana fada da gwamnatin Senegal wanda ya kai ga mabanbantan zanga-zanga da kame da ma kisan tarin fararen hula yayin arangamar da suka rika da jami’an tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu