Isa ga babban shafi

Yau ake rantsar da sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye

Yau Talata ake bikin rantsuwar kama aikin sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye, wanda zai maye gurbin shugaba mai barin gado Macky Sall da ya shafe tasawon shekaru 12 ya na mulkin kasar ta yammacin Afrika, tun daga shekarar 2012 zuwa 2024.

Sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye tare da shugaba mai barin gado Macky Sall.
Sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye tare da shugaba mai barin gado Macky Sall. AFP - -
Talla

Shugabannin kasashe daga ciki da wajen nahiyar Afirka ne ke halartar taron bikin rantsuwar kama aikin sabon shugaban kasar na Senegal mai shekaru 44, cikinsu kuma har da shugaban Najeriya, kuma shugaban kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS Bola Ahmed Tinubu.

A yayin da sabon shugaba Bassirou Diomaye Faye ke kama aiki daga wannan Talata, masu bibiyar lamurran Senegal ciki da wajenta na cigaba da tofa albarkacin bakinsu akan manufofin da suke fatan sabon shugaban zai gabatar, da kuma tarin kalubalen da ke gabansa na kawar da wasu matsaloli da ke ci wa kasar tuwo a kwarya.

Daga cikin manyan batutuwan akwai kokarin kawo karshen matsalar tsadar rayuwa a Senegal, da yakar cin hanci da Rashawa da kuma sulhunta bangarori da baraka ta kunno kai tsakaninsu a siyasance, sai kuma uwa uba, kawar  da matsalar rashin ayyukan yi, matsalar da masana ke fargabar mai yiwuwa a dauki lokaci kafin cimma nasarar kawo karshenta lura da cewar tilas tsarin tattalin arzikin kasar ta Senegal na neman sauye-sauye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.