Isa ga babban shafi

Ɗan shugaban kasar Uganda ya sha alwashin yakar rashawa tsakanin sojoji

Dan shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi alkawarin yakar cin hanci da rashawa a ma’aikatar tsaron kasar kwanaki bayan ya karbi ragamar jagorancin rundunar, matakin da ake kyautata zaton hanyar gadon mahaifinsa ne.

Ɗan shugaban kasar Uganda Muhoozi Kainerugaba wanda ke jagorantar sojojin kasar. 7/05/2022
Ɗan shugaban kasar Uganda Muhoozi Kainerugaba wanda ke jagorantar sojojin kasar. 7/05/2022 AP - Hajarah Nalwadda
Talla

A makon jiya ne, Museveni, mai shekaru 79, wanda ya jagoranci Uganda tsawon shekaru 38, ya nada dansa Muhoozi Kainerugaba mai shekaru 49 a matsayin sabon babban hafsan hafsoshin tsaron kasar da ke gabashin Afirka.

A wani bikin mika mulki a hukumance a ranar Alhamis, Kainerugaba "ya sha alwashin inganta jin dadin sojoji ta hanyar yaki da muggan laifuka da almubazzaranci da dukiyar kasa, Kamar yadda wata sanarwa da rundunar ta fitar ta nuna.

Gabashin Afirka

Sojojin Uganda na taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a yankin kuma na da dakaru da aka girke a Somaliya da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo inda sojoji ke taimakawa wajen yakar masu kaifin kishin Islama.

'Yan adawar Uganda sun zargi Museveni da bin diddigin al'amuran soja da nufin kimtsa dansa ya ya karbi mulki a siyasance.

A shekarar 2022, Museveni ya cire Kainerugaba daga mukaminsa na kwamandan sojojin kasa na Uganda bayan ya yi barazanar mamaye makwabciyarta Kenya a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.