Isa ga babban shafi
JUYIN MULKI

ECOWAS na duba yuwuwar janye takunkumin da ta sanyawa wasu kasashen yammacin Afirka

Shugabannin kungiyar kasashen yammacin nahiyar Afrika, ECOWAS/CEDEAO za su yi wani taro a cikin karshen wannan makon don nazari kan takunkuman da aka kakaba wa kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar.

Taron ECOWAS karo na 64 da ya gudana a Abujan Najeriya ranar 10 ga Disamban 2023, inda aka tattaunawa kan juyin mulkin kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Nijar.
Taron ECOWAS karo na 64 da ya gudana a Abujan Najeriya ranar 10 ga Disamban 2023, inda aka tattaunawa kan juyin mulkin kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Nijar. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Wasu majiyoyi sun ce akwai yiwuwar janye takunkuman da aka sanya wa kasashen, da zummar jan hankulansu su yi mi’ara a kan matakin da suka dauka na ficewa daga kungiyar, wanda suka dauka a watan Janairu, biyo bayan takun saka da suka shiga sakamakon juyin mulki a kasashen nasu.

Da yake jawabi ga manema labarai gabanin taron da za a yi a Abujan Najeriya, babban jakadan kungiyar tarayyar Afirka ta AU, Muhammad Ibn Chambas, ya yi kira ga gwamnatocin sojin kasashen Mali, Burkina Faso, da kuma Nijar, da su janye matakin su na ficewa daga kungiyar.

Chambas ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki, da su karbi kiran da tsohon shugaban gwamnatin sojin Najeriya, Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya yi, na kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin ECOWAS da adannan kasashe, tare da hada kan al'ummar yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.