Isa ga babban shafi

Kasar Benin ta janye dakatar da shigar da kayayyaki zuwa kasar Nijar

Babban daraktan tashar jiragen ruwan Benin ya bayyana cewa kasar ta janye dakatarwar da ta yi na kayayyakin Nijar da ake shigar da su ta tashar ruwan Cotonou, bayan shafe watanni biyar sakamakon takunkumi da kungiyar ECOWAS/CEDEAO ta kakabawa kasar.

Tashar jiragen ruwan Benin
Tashar jiragen ruwan Benin © Prospoer Dagnitche / AFP
Talla

Kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS/CEDEAO ta kakabawa Nijar takunkumin ne bayan juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli da sojoji suka hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Matakan sun kai ga rufe kan iyakar kasar da Benin, inda aka samu katsewar samun kudaden shiga bayan da aka dakatar da jigilar kayayyaki zuwa Nijar ta tashoshin jiragen ruwa.

Babban daraktan tashar Bart Jozef Johan Van Eenoo ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta dage matakin da ya shafi dakatar da kayayyakin da ake shiga da su Nijar daga tashar ruwan na Cotonou.

Ya kara da cewa, an dauki matakin ne a kokrinsu na ci gaba da gudanar da hada-hadar kayayyaki a tashar jiragen ruwa na Cotonou, musamman domin rage cunkoso da ake fuskanta a tashar.

Matakin na zuwa ne kusan mako guda bayan da shugaban kasar Benin Patrice Talon ya yi kira da a gaggauta sake kulla dangantaka tsakanin kasarsa da makwabciyarta Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.