Kungiyar Francophonie ta kori Nijer daga cikinta.
Komitin dindindin na kungiyar Francophonie (CPF) ya dakatar da jamhuriyar Nijer daga cikin kungiyar, tare da bukatar ganin sakataren kungiyar, ya ci gaba da tuntubar mahukumtan na Nijer, da zummar tsayar da ruwan miya kan batun komawar kasar kan tafarkin demokradiya, kamar yadda kungiyar ta OIF bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya juma’a.
Wallafawa ranar:
A dai gefen kuma kungiyar Ecowas ko Cedeao a makon da ya gabata, ta yi wata ganawa da mahukumtan jamhuriyar Nijer, karkashin jagorancin shugaban kasar Togo ta bayyana cewa, bangarorin biyu sun cimma matsaya kan batutuwan da zasu tattauna a kai, da suka hada da wa’adin da sojoin za su dauka a karkashin gwamnatin ta rikon kwarya kasar
Tattaunawar bangarorin biyu dai ta ta’allaka ne kan battun wa’adin mulkin rikon kwaryar, bayan da tun farkon da farko bayan juyin mulkin sojoji suka bayyana, kebewa kansu wa’adin shekaru 3 kafin su mika Mulki ga hannun wata gwamnatin farar hula
Sai dai ita kuma kungiyar ta CEDEAO ta kafe ne, a tsakanin watanni 15 zuwa 18 na wa’adin rikon kwaryar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu