Zazzabin Dengue ya kashe sama da mutane 214 a Burkina Faso cikin wata 10
Mahuknata a Burkina Faso sun ce wata cuta da sauro ke yadawa da ake kira zazzabin Dengue ya lakume rayuka dari 2 da 14 tun daga ranar 1 ga watan Janairun wannan shekara, akasari a birnin Ouagadougou da Bobo-Dioulasso, birin na biyu mafi girma a kasar.
Wallafawa ranar:
Cikin wata sanarwa ma’aikatar lafiyar kasar da ke yammacin nahiyar Afrika ta ce daga ranar 1 ga watan Janairun wannan shekarar zuwa 15 ga watan Oktoba an samu mutane dubu 50 da dari 4 da 78 da suka harbu da wannan cuta, inda daga cikin su mutane 214 suka mutu.
Yaduwar cutar cikin sauri
Sanarwar ta ce daga ranar 9 zuwa 15 ga watan Janairu shekarar 2023 kawai sama da mutane dubu 10 ne suka kamu da wannan cuta, aka samu mace-mace 48, kuma biranen Ouagadougou da Bobo-Dioulasso ne wannan cuta ta fi kamari, a cewar ministan lafiya, Robert Lucien Jean-Claude Kargougou.
kamanceceniya da zazzabin Malaria
Zazzabin Dengue, wanda sauro ne ke yadawa, yana da alamomi masu kamanceceniya da zazzabin Malaria, wanda ke yaduwa a kasashen da ake da yanayi na zafi, inda yake kama mutane miliyan 100 zuwa 400 a duk shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
A shekarar 1960 ce wannan cuta mai sanya zazzabi mai zafi, ciwon kai, jiri da amai, wani lokacin ma zubar jini ta fara bulla a Burkina Faso, amma a shekarar 2017 ce aka mayar da hankali a kanta, bayan ta kashe mutane 17.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu