Isa ga babban shafi

Tsananin zafi ya ta'azzara karuwar masu zazzabin Dengue a Duniya- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta yi gargadi kan yiwuwar karuwar masu kamuwa da zazzabin Dengue a sassan Duniya sakamakon tsananin zafin da ake gani a wasu sassa cikin watan nan.

Zazzabin Dengue na sahun cutuka masu hadari.
Zazzabin Dengue na sahun cutuka masu hadari. © Rithea Leang
Talla

Raman Velayudhan shugaban sashen kula da cutukan da duniya ke kawar da kai akansu a hukumar ta WHO ya shaidawa taron manema labarai na birnin Geneva cewa yanayin da ake ciki yanzu na tsananin zafi a galibin kasashe zai haddasa fantsamuwar kwayoyin cutar ta Dengue mai hadari.

A cewar jami’in tsananin zafin baya ga fari mai tsayi ya jefa rayuwar rabin al’ummar duniya a hadarin kamuwa da cutar bayan da ta fantsama kasashe 129.

Velayudhan ya bayyana cewa duk shekara mutane akalla miliyan 100 zuwa miliyan 400 na kamuwa da cutar ta Dengue inda a Amurka kadai ake samun mutane miliyan 2 da dubu 800 masu harbuwa da cutar duk shekara wadda zuwa yanzu ta kashe mutane dubu 101 da 280.

Zazzabin na Dengue da ke sahun cutukan da sauro ke yadawa masana bangaren lafiya na sanya shi a sahun cutuka masu matukar hadari ga bil’adama lura da yadda ya ke ci gaba da kisa shekara bayan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.