Isa ga babban shafi

Fiye da dalibai mata 90 sun harbu da wata nau’in cuta da ta barke a Kenya

Ma’aikatar lafiya a Kenya, ta tabbatar da harbuwa fiye da dalibai mata 90 da wata cuta da ta ce ba a kai ga gano ko wacce iri ba ce, lamarin da ya kai ga kwantar da su a asibiti.

Har yanzu dai ba a kai ga gano nau'in cutar ba, sai dai ta kwantar da 'yan matan da yawansu ya haura 90.
Har yanzu dai ba a kai ga gano nau'in cutar ba, sai dai ta kwantar da 'yan matan da yawansu ya haura 90. REUTERS - BAZ RATNER
Talla

Mahukuntan kwalejin mata ta Eregi Girls High School da ke yammacin Kenya sun tabbatar da harbuwar tarin matan su fiye da 90 wadanda galibinsu suka faro ciwon gwiwa sai kuma gaza iya tafiya tare da mutuwar jiki.

Jami’an ma’aikatar lafiyar Kenya da suka kai ziyara makarantar sun tabbatar da daidaituwar lamurra tare da fatan dawowar karatu bayan shawo kan cutar.

Shugaban sashen ilimi na yankin yammacin Kenya Jared Obiero, ya ce an dauki nau’in fitsari da jinin daliban da suka harbu da cutar don gudanar da bincike da nufin tabbatar da nau’in cutar da ke damunsu.

A cewarsa sai bayan gudanar da bincike ne za a tabbatar da cutar dama dalilin da ya haddasa ta, dai dai lokacin da ya sha alwashin bayar da cikakkiyar kulawa ga wadanda suka harbu da cutar har zuwa warkewarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.