Isa ga babban shafi

Katse tallafin Faransa ya jefe al'ummar Nijar da Burkina Faso a matsanancin kunci

Yau kimanin watanni biyu kenan da Faransa ta dakatar da tallafin ci gaban da  ta ke baiwa gwamnatocin kasashen jamhuriyar Nijer da Burkina Faso. Tallafin da aka kiyasta da cewa, ya kai kimanin na Euro miliyan 200.A yau assabar kungiyoyin bayar da agajin jinkan sun gabatar da kashedin cewa, rashin  wannan tallafi, zai iya dakatar da daruruwan ayukan jinkai ga al’ummomin karkarar wadannan kasashe.

Une marchande de fruits sur le marché de Bobo-Dioulasso, la capitale économique du Burkina Faso. (Image d'illustration)
Une marchande de fruits sur le marché de Bobo-Dioulasso, la capitale économique du Burkina Faso. (Image d'illustration) AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Duk da cewa, an baiwa  kungoyin agajin Faransa damar ci gaba da gudanar da ayukansu a jamhuriyar Nijer da  Burkina Faso, da dama sun tsayar da aiki, saboda dakatar da kudaden tallafin tafiyar da ayukansu da Faransar ta yi.

Olivier Bruyeron, shugaban hadadiyar kungiyar  SUD da ta hada kungiyoyin bayar da agaji sama da 180 na duniya,  ya bayyana  matukar damuwarsa kan soke tallafin kamar haka.: « a hakikanin gaskiya dukkanin ayukan jinkai ne ke fuskantar barazanar tsayawa. Ana maganar ayukan jinkai ne dake tafiya da yanayin da ayukan gona da kuma aikin sauyin yanayi suka sama, ana maganar harakokin kiyon lafiya, da ayukan ci gaba n ilimi, da dai sauransu. don haka a kwai ayuka masu matukar muhimmanci dangane da ci gaban rayuwar dubban al’umar kasar ta Nijer. Muna bukatar  fita cikin wannan  yanayi mai matukar hazo, a hakikanin gaskiya a cikin wasu kwanaki ko makwanni masu zuwa lamarin zai iya kara kazancewa. »

Kungiyoyin masu zaman kansu sun bayyana matukar  damuwarsu, ta yadda suke nazarin irin mummunan yanayin da tsaida ba da tallafin ci gaban da  Faransa ta yi, ya jefa kasar Mali a ciki, tun cikin watan mayun da ya gabata.

Frédéric Apollin, daraktan wata kungiyar agaji ya ce :  « mun ga  misali a yankin arwacn kasar Mali : inda   ayarin jami’an kiyon lafiya, ke aiki warkar da al’umma guda maza da mata a  lokaci guda, da kuma kula da lafiyar dabbobi dake kai kawo a yankunan kiyon dabbobi. Aikin da wata kungiya bayar da agaji ta kasar Mali ke tafiyarwa, yau kuma, ba ta da kudin da za ta iya gabatar da wannan aiki. A kan haka wadannan ayuka dake amfanar da sama da iyalai dubu 30 yau shekaru biyu ke nan da suka gabata da aikin ya tsaya.».

Kungiyoyin bayar da agajin dai sun yi kira ga gwamnatin Faransa da ta sake maido da tallafin kudin ga kasashen Burkina Faso da jamhuriyar Nijer, kasashen da aka bayyana cewa, kimani mutane miliyan 18 na bukatar tamakon jinkan gaggawa a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.