Isa ga babban shafi

Al-Shabaab ta hallaka sojoji 54 a wani hari da ta kai Somalia

kungiyar Al-Shabaab mai ikrarin jihadi a Somalia ta kashe dakarun tabbatar da zaman lafiya da dama a wani mummunan harin da ta kai a kasar.

Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia
Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia RFI-Swahili
Talla

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya baiyana cewa sojoji 54 ne suka mutu a Somalia a makon da ya gabata yayin wani mummunan hari da ‘Yan kungiyar Al-Shabaab da ke ikrarin jihadi suka aikata a kasar da yaki ya dai-daita.

Shugaban ya kuma kara da cewa an samu damar gano gawarwakin sojoji 54 wanda ya hada da wani kwamandansu.

Fadar shugaban kasar ta baiyanawa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa shugaban yayi wannan jawabi ne ga kwamitin zartaswar jam’iyar NRM mai mulki a kasar a ranar lahadi.

Harin yayi muni ne sakamakon wanda dakarun da ke marawa gwamnati baya da ke samun goyon bayan Kungiyar AU ATMIS ta kaiwa kungiyar Al-Shabaab a watan Agustan shekarar data gabata.

Kungiyar Al-Shabaab da ta shafe fiye da shekaru 10 tana kai munanan hare-hare kan gwamnatin Somaliya inda kuma ta dauki alhakin harin na ranar 26 ga watan Mayu, sansanin kuma kashe sojoji 137.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.