Isa ga babban shafi

Sabbin dokokin tsaurara hukunci kan masu auran jinsi sun fara aiki a Uganda

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ratttaba hannu kan wasu sabbin dokokin hukunta masu laifin auren jinsi daya a kasar, wadanda aka bayyana su a matsayin mafiya tsauri da aka gani a duniya.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni.
Shugaban Uganda Yoweri Museveni. AP - Bebeto Matthews
Talla

Tuni dai wasu manyan kasashen yammacin Turai da Amurka gami da wasu kungiyoyin masu rajin kare hakkin masu auren jinsin suka fara caccakar gwamnatin kasar ta Uganda.

A farkon watan Mayu ‘yan majalisar Uganda suka amincce da dokokin na tsaurara hukunci ciki kuwa har da kisa ga dukkanin wadanda aka kama da laifin dabi’ar auren jinsi daya, inda suka kuma sha alwashin bijirewa duk wani matsin lamba, da kokarin yi musu katsalandan daga kasashen ketare.

Yayin mayar da martani kan kunshin dokokin na Uganda, shugaban Amurka Joe Biden yayi barazanar katse tallafin kudade da kuma zuba hannayen jarin da yake wa kasar, bisa abinda ya kira tauye hakkin dan adam din da yayi muni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.