Isa ga babban shafi

Ba zan daina koran ma'aikata da rushe-rushe a Kaduna ba- Nasir El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai na Jahar Kaduna a Najeriya ya ce ba zai gaza ba wajen cigaba da sallamar ruba-ruban ma’aikata da kuma rushe gine gine ba har zuwa ranar karshen wa’adin mulkin sa. 

Gwamnan jihar Kaduna.
Gwamnan jihar Kaduna. © Twitter/Nasir El-Rufai
Talla

Gwaman, ya baiyana haka ne a yayin taron kaddamar da wani littafi da aka wallafa akan irin kokari da ya yi a kan kujerar sa ta gwamna, a lokacin da ake sauran kwanaki kadan ya bar kujerar. 

Littafin dai mai taken "Putting People First" ma'ana, 'amfanar da al’uma shine mulki', wani gogaggen dan jarida kuma mai sharhi a kan lamuran yau da kullum Mista Emmanuel Ado ne ya wallafa. 

Gwamna El-Rufai ya ci gaba da cewa ya yi kokarin barin baya da kyau a dukkanin tsare tsaren da ya yi na jagoranci a jihar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.