Tarayyar Turai ta gargadi Burundi
Ministocin Kungiyar kasashen Turai sun ce a shirye suke su sake kakabawa kasar Burundi Karin takunkumin kariyar tattalin arziki sakamakon kasa kulla yarjejeniyar kawo karshen tashin hankalin da ake samu a kasar wanda yanzu haka ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 440.
Wallafawa ranar:
Tarayyar Turai ta bayyana damuwa kan rashin mutunta yarjejeniyar Cotonou.
Akwai dai Hukumar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International da tace ta gano wasu manyan kaburbura guda biyar a kusa da Bujumbura inda jami’an tsaron Burundi suka binne gawarwakin mutanen da suka kashe.
Burundi ta fada cikin rikici tun a watan Afrilun 2015 lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya ayyana matakin neman wa’adin shugabanci na uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu