Isa ga babban shafi
Rwanda

Rwanda za ta sallami 'yan gudun hijirar Burundi

Gwamnatin Rwanda ta ce za ta sallami ‘yan gudun hijirar Burundi fiye da dubu 75 da ke zaman gujewa rikicin kasar a dai dai lokacin da Burundin ke zargin Rwanda da hannu wajen rura rikicin kasar.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijrar Burundi da ke neman mafaka a Rwanda
Wasu daga cikin 'yan gudun hijrar Burundi da ke neman mafaka a Rwanda AFP PHOTO / STEPHANIE AGLIETTI
Talla

A cikin wata sanarwar da ta fitar, Rwanda ta ce, nan bada jimawa ba, za ta fara shirin tura ‘yan gudun hijirar zuwa wasu kasashen dabam cikin tsanaki.

To sai dai hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijra ta majalisar dinkin duniya ta bayyana damuwarta akan matakin tare da fadin cewa, hakan tamkar warware tsarin kare ‘yan gudun hijira ne da Ruwandan ta fara shekaru da dama da suka gabata.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.