Isa ga babban shafi
Najeriya

Dillalan man fetur sun janye yajin aiki a Najeriya

Kungiyar dillalan Man fetur a Najeriya sun dakatar da yajin aikin su na sai baba ya gani, wanda ya jefa al’ummar kasar acikin mawuyacin hali, bayan haifar da nakasu ga tattalin arzikin kasar.Kungiyar da ke raraba man fetri da iskar gas ta sanar da janye yajin aikin ne, bayan kammala wata zaman tattaunawa da ‘yan majalisar dattawa kasar.

NNPC.
NNPC. Getty Images/Suzanne Plunkett
Talla

Matsalar karancin man fetur a Najeriya ya haifar da koma baya a bangarori da dama, inda a halin yanzu masu ababan hawa, kamfanoni da masana’antu suka shiga mawuyacin hali sakamakon rashin mai.

Ita ma dai Jam’iyyar APC da ke shirin karbar mulki a Najeriya, ta zargi shugaban kasar mai barin gado Goodluck Jonathan da cewa zai danka ragamar mulki ne a cikin mummunan yanayi da kasar ba ta taba samun kanta a cikinsa.

Jam’iyyar ta bayar da misali da matsalar karancin wutar lantarki, da yajin aiki da kuma basusuka na sama da dala milyan dubu sittin da ake bin gwamnati a cikin gidan kawai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.