Isa ga babban shafi
Najeriya

Baki na tserewa daga jihar Ekiti a kudancin Najeriya bayan wani rikici

Hukumomi a jihar Ekiti dake yankin kudu maso yammacin Najeriya sun sanya dokar takaita zirga zirga, bayan wani tashin hankalin da aya auku a jihar. Rahotanni na cewa wasu drebobi ne suka far wa baki a ranar Laraba da ta gabata, ta hanya sara adduna, lamarin da yayin sanadioyyar rasa ran a kalla mutane 3.Bayanai na nuna cewa zuwa yanzu baki na ci gaba da kauracewa jihar, sai dai gwamnan jihar Ayo Fayose, ya baiwa jama’a tabbacin kiyaye doka da oda.Sai akwai rahotannin dake cewa wasu bata gari suna ci gaba da fashe gidaje da shagunan baki, inda suke kwashe kayayyakin dake ciki.Bello Garba, ne dan madamin jihohin yamma a fadar mai martaba Sakin Shashan Ibadan Haruna mai Yasin, ya kuma yi kira ga hukumomin kasar su gaggauta yin bincike kan lamarin. 

Jami'an tsaro suna bakin aiki a Najeriya
Jami'an tsaro suna bakin aiki a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.