Nkurunziza ya jaddada aniyarsa ta yin tazarce a Burundi
Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya shaidawa al’ummar kasar cewar zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi a watan gobe, a dai dai lokacin kasashen duniya ke gargadin ya kaucewa matakin. Tuni shugabannin kasashen da ke Gabacin Afirka suka kira taron gaggawa a makon gobe don tattaunawa kan matsalar wadda tuni ta haifar da ‘yan gudun hijira sama da 40,000 da suka bar kasar zuwa Rwanda.
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya tace mutanen kasar Burundi sama da 21,000 suka tsere zuwa kasar Rwanda tsakanin Assabar zuwa Lahadi saboda fargabar rikicin siyasa a cikin kasar.
Tun a farkon watan Afrilu ne Jam’iyyar CNDD mai mulki ta ba shugaban kasa Pierre Nkurunziza damar neman wa’adi na uku a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 26 ga watan Yuni.
Tun a 2005 ne shugaban ke jagorantar kasar, yayin da ‘yan adawa ke bayyana cewa matakin tazarcen ya sabawa kundin tsarin mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu