Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta kaddamar da binciken dalilin kisan Sojojinta

Majalisar Tsaron Jamhuriyar Nijar ta bukaci kaddamar da bincike kan harin da mayakan Boko Haram suka kai wa sojojin kasar inda aka ruwaito cewar akalla 48 daga cikin su sun mutu. Bayan wani zama na musamman da majalisar ta yi jiya, ta amince da tura jami’anta inda aka kai harin dan tabbatar da sahihancin abin da ya faru.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou France 24
Talla

Rahotanni masu karo da juna na cewar adadin sojojin da ka aka kashe ya zarce 50 amma gwamnatin tace ba zata ce komai ba sai ta kammala bincike akai.

Majiyoyin tsaro a Chadi sun tabbatar da cewa sojojin Nijar da dama ne mayakan Boko Haram na Najeriya suka kashe a gabar tabkin Chadi.

Wata Majiyar tace kimanin Sojojin Nijar 48 aka kashe, sannan 36 suka bace, amma wasu da dama sun samu tserewa.

Amma Wata majiyar tsaron daga yankin Diffa da ke kan iyaka da Najeriya ta tabbatarwa kamfanin dillacin Labaran Faransa cewa adadin Sojojin da aka kashe sun kai 80, yayin da 30 daga cikinsu bas an inda suka shiga ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.