Isa ga babban shafi
Nijeriya,kaduna

Al’amurra sun tsaya cik a Kaduna yayin da ake dakon sakamakon zabe

Yayin da ake ci gaba da dakon sakamakon zaben Najeriya da aka yi a karshen mako, harkokin yau da kullum sun tsaya cik a birnin Kaduna.

Mata masu dakon sakamakon zaben Najeriya
Mata masu dakon sakamakon zaben Najeriya REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

A cikin Rahoton da Garba Aliyu ya aiko, wani mazaunin Kaduna Nuhu Abdullahi mai sana’ar facin taya a Jihar ya ce mutane sun saba da yanayin a canza musu Kuri’unsu, lamarin da a karshe ke haifar da rikici, wannan dalilin ne ya sa kowa ya kama kansa a gida domin gujewa rikicin bayan zabe.

Alhaji Ibrahim mai siyar da Jaridu yana ganin mutane na tsoron kar su fito wani abu ya auku, mutum ya kasa komawa gida.

Wakilinmu Garba Aliyu Zaria ya rawaito cewa an rufe makarantu da dama sakamakon furgabar abin da ka iya biyo bayen sanar da sakamakn zaben da aka gudanar a ranar Assabar har zuwa Lahadi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.