Isa ga babban shafi
Kamaru-Najeriya

‘Yan Bindiga sun sace mutane 15 da Magajin gari a Kamaru

Wasu ‘yan Bindiga dadi a kasar Kamaru, sun sace mutane 15 da suka hada da wani Magajin gari da jami’an karamar a yankin kan iyakar kasar da kasar Chadi

Soldats tchadiens déployés dans le cadre de la force militaire mixte contre Boko Haram, au Nigeria, en février 2015.
Soldats tchadiens déployés dans le cadre de la force militaire mixte contre Boko Haram, au Nigeria, en février 2015. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Hukumomin kasar ta Kamaru sun bayyana ceware ayarin mutanen da aka sace, sun tafi ne domin binne wani ammaci a wata Makabarta ta Garoua-Boulai mai nisan kilomita 600 Arewa maso gabashin birnin Yaounde na kasar ta Kamaru.

Dai daga cikin mutanen da aka kama ya kubuta, ya bayyana cewar an shiga da mutanen ne a yankin kasar Jamhuriyar Afruka ta tsakiya.

Wannan al’amarin kuma na faruwa ne a yayin da ake dada samun fargabar sulalewar ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da ke fuskantar karin kai hare-haren Dakarun gwamnatocin kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar.

A kwanan nan dai shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan na bayyanawa Duniya cewar sun kusa murkushe kungiyar Boko Haram, bisa alkawarin da suka yi na kammala fada da kungiyar a cikin Makonni 6 da aka kara na wa’adin gudanar da zaben shugaban kasa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.