Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Sojojin Najeriya sun yi ikirarin kwato garuruwa 30

Rundunar Sojin Najeriya tace dakarunta sun yi nasarar kwato garuruwa 30 da ke hannun Mayakan Boko Haram, kuma daruruwan mayakan ne aka kashe. Wannan na zuwa ne a yayin da Dakarun kasar Chadi suka bayyana nasasar kwato garin Dikwa bayan sun fatattaki Mayakan Boko Haram.

Garin Dikwa da Dakarun Chadi suka kwato
Garin Dikwa da Dakarun Chadi suka kwato Nako Madjiasra / RFI
Talla

A cikin sanarwar da Hedikwatar Sojin Najeriya ta fitar a Twitter ta bayyana cewa Sojojin kasar sun kwato Gujba da Geri da Kukawa a Jihar Yobe da kuma Gulak da Madagali a Adamawa.

Sauran garuruwan sun hada da Monguno da Marte da Baga da Gamboru Ngala da Dikwa da Kamla da Bumsa da Buza da Tetebah da Shikah da Fikayel a Jihar Borno.

Bayan kwato garuruwan daga hannun Boko Haram, Sanarwar tace yanzu Sojojin Najeriya za su mayar da hankali wajen tabbatar da tsaro a yankin domin ba mutane damar tafiyar da rayuwarsu ba tare da wani fargaba ba.

Dakarun kasar Chadi sun yi nasasar kwace ikon garin Dikwa bayan sun fatattaki Mayakan Boko Haram da suka karbe ikon garin, lamarin da ya kai ga kisan Sojan kasar guda.

Kwamandan sojan kasar Kanar Azem Bermandoua ya ce yanzu haka garin Dikwa na hannunsu bayan sun kashe mayakan kungiyar da dama.

Wakilin kanfanin dillancin labaran Reuters da ke tare da dakarun ya ce akasarin mutanen garin sun gudu tun bayan fadawa hannun mayakan kungiyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.