Isa ga babban shafi
Najeriya

"Sai an sauya doka kafin ‘Yan gudun hijira su shiga zaben 2015"

Hukumar zabe a Najeriya tace har sai an sauya dokar zaben kasar kafin dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya sa suka tserewa gidajensu su iya shiga babban zaben 2015 da za a gudanar a watan Fabrairu.

Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega RFI/Bashir
Talla

Mai Magana da yawun shugaban hukumar zaben ne Kayode Idowu ya bayyana haka, yana mai cewa muddin ba a sauya dokar ba, Jam’iyyar da ta fadi zaben na iya kai kara kotu.

Jami’in ya ce suna fatar yan majalisun kasar zasu sauya dokar cikin hanzari don bai wa wadanda suka tserewa matsuguninsu damar shiga zaben.

Sama da mutane Miliyan guda ne a Jihohin arewa maso gabacin Najeriya suka zama ‘Yan gudun hijira saboda hare haren Mayakan Boko Haram.

Dokar zabe a Najeriya tace ‘Yan kasar za su kada kuri’a ne a yankinsu, don haka dole sai Majalisa ta canza dokar domin ba wadanda suka gujewa rikicin Boko Haram damar kada kuri’unsu a zaben.

Masu lura da siyasar Najeriya sun bayyana cewa zaben 2015 zai kasance mafi zafi fiye da zabukan da suka gabata tun kawo karshen mulkin soja a 1999.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP zai fafata ne da Tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari dan takarar Jam’iyyar adawa ta APC a zaben 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.