Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

An saki Lazarevic Bafaranshen da aka sace a Mali

Shugaban Faransa Francois Hollande yace an saki Bafaranshe Serge Lazarevic, da aka sace a Mali a 2011 wanda kuma yanzu shi ne mutumin Faransa na karshe da aka yi garkuwa da shi a wata kasa a duniya.

Bafaranshe Serge Lazarevic tare da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a birnin Yamai bayan sakinsa daga hannun Mayakan Al Qaeda a Magrib
Bafaranshe Serge Lazarevic tare da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a birnin Yamai bayan sakinsa daga hannun Mayakan Al Qaeda a Magrib AFP PHOTO / HAMA BOUREIMA
Talla

A yau Talata ne shugaban Faransa ya tabbatar da sakin Bafaranshen wanda shi ne na karshe da ake garkuwa da shi a wata kasa bayan Mayakan Algeria sun fille kan hiker Herve Gourdel.

A shekarar 2011 ne aka yi garkuwa da Serge Lazarevic, wanda dan asaln Faransa ne da Serbia.

Faransawa kimanin 15 ne aka yi garkuwa da ssu yawanci a Nahiyar Afrika a tsakanin 2013.

Mayakan Al Qaeda ne reshen Mgreb suka yi garkuwa da Lazarevic da Philippe a ranar 24 ga watan Nuwamba a lokacin da ya je yawun kasuwanci a Mali.
A bara ne kuma aka tsinci gawar Philippe.

Babu dai wani bayani akan yadda aka saki Bafaranshen, amma shugaba hollande ya godewa Mali da Nijar da suka taimakawa wajen sakin Lazarevic.

Kuma yanzu an bayyana cewa yana kan hanyarsa ta zuwa Faransa daga Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.